Zaben 2023: Babban sirrin ya tonu game da boyayyen dabarar da Peter Obi ya yi wa APC, PDP da wasu

Zaben 2023: Babban sirrin ya tonu game da boyayyen dabarar da Peter Obi ya yi wa APC, PDP da wasu


Victor Umeh, jigo a jam'iyyar Labour ya bayyana cewa sansanin jam'iyyar APC mai mulki da na PDP sun shiga rudani sakamakon karuwar farin jinin Peter Obi.

Umeh wanda dan takarar kujerar sanata ne a karkashin inuwar jam’iyyar Labour a jihar Anambra ya bayyana haka yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Television, Sunrise Daily a ranar Laraba, 14 ga watan Satumba.

A cewar wani rahoto da gidan Talabijin na Channels, jigo a jam’iyyar Labour ya ce yana da kwarin gwiwar cewa wasu ‘yan PDP da APC za su zabi Peter Obi a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Umeh ya ce:

“Na san akwai mutane a PDP da za su zabi jam’iyyar Labour. Na san akwai mutane a APC da za su zabi jam’iyyar Labour. Abin da ke da muhimmanci shi ne aikin ceto Najeriya kuma mutane ba su yarda cewa wannan abu na iya aiki a wajen wannan dandali ba."

NLC za ta iya cirewa Peter Obi kuri'u miliyan 12 - Victor Umeh

A halin da ake ciki, Umeh ya kuma mayar da martani ga alkawarin da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta yi na tara masu zabe miliyan 12 a fadin kananan hukumomi 774 domin yiwa Peter Obi.

Umeh ya ce kungiyar ta NLC tana da sahihin tsarin da za ta cire ta kuma za ta zama wata dama ce a gare su wajen karfafa kungiyar da kuma kawo karshen dogon wahalhalu a hannun gwamnatocin baya.

A yayin da yake mayar da martani kan zarge-zargen da jam’iyyar adawa ta yi na cewa jam’iyyar Labour ba ta da tsari, Umeh ya ce:

“Mutanen sauran jam’iyyun yanzu sun firgita. Da farko dai suna ta zage-zage na cewa jam’iyyar ba komai ba ce.

"Yau jam'iyyar Labour ta zama mafarkin su, me ya faru, Labour Party suna raba kudi, Labour Party ba ta raba kudi."

Umeh ya ci gaba da bayyana cewa Peter Obi bai yi kasa a gwiwa ba wajen tuntubar sa a yunkurinsa na lashe zaben shugaban kasa.

Ya ce tuntubar Obi ta shafi dukkan shiyyoyin kasar nan kuma ba shakka za ta haifar da sakamako mai kyau da tasiri.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN