DA DUMI-DUMI: An tsige shugaban jam'iyyar APC a jihar Arewa mai karfin siyasa

DA DUMI-DUMI: An Cire Shugaban Jam'iyyar APC A Jihar Arewa Mai Karfi 


Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya dauki sabon salo, yayin da reshenta na jihar Adamawa ya tsige shugaban jam’iyyar, Ibrahim Bilal.

Daily trust ta ruwaito cewa Bilal yana da hannu a cikin ayyukan cin hanci da rashawa, da karkatar da kudi, da kuma saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Nan take aka rantsar da Ismaila Tadawus, mataimakin Bilal a matsayin sabon shugaban jam’iyyar a jihar yayin da jami’ai 24 daga cikin 36 suka rattaba hannu.

Kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC ya zargi shugaban jam’iyyar da karbar kudi a wani taro a sakatariyar jam’iyyar a Yola, babban birnin jihar a ranar Litinin, 5 ga watan Satumba.

Hakan na kunshe ne a cikin jawabin da sakataren yada labaran jam’iyyar a jihar, Mohammed Abdullahi ya karanta, inda kwamitin ya kuma yi zargin cewa shugaban jam’iyyar ya yi zamansa a sakatariyar har na tsawon watanni biyu, kuma ba ya nan a fili a zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar.

Abdullahi ya ci gaba da cewa Bilal ya ki amsa zargin da ake masa.

Ya kaurace wa zamansa na Abuja lokacin da jam’iyyar ke aikin sasanta ‘ya’yanta da kuma magance korafe-korafen da ke tsakanin shugabannin jam’iyyar.

Sanarwar ta kara da cewa, “Shugaban ya boye kudaden jam’iyyar kuma yana tafiyar da al’amuran jam’iyyar tamkar wani jari ne na kashin kansa ba tare da tantancewa ba kuma ba tun lokacin da ya hau kan karagar mulki”.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN