An kama budurwar 'yan bindiga da masu ba su labarin sirri a Kaduna


Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da cafke wasu ‘yan mata biyu da aka ce masu ba yan ta'adda bayanan sirri ne da kuma budurwar ‘yan bindiga a kauyukan Maraban-Jos da Rigachikun da ke karamar hukumar Igabi a jihar.

Wadanda ake zargin mai suna Hafsat Ibrahim da Rabi Bala, an kama su ne tare da wani mai ba da labari mai suna Bayero Adamu, daga hannun jami’an hukumar ‘yan banga ta jihar Kaduna (KADVS) da ke aiki a cikin al’ummomin, inda suka mika su ga rundunar ‘yan sandan jihar domin gudanar da bincike.

Da yake tabbatar da kamun, kakakin rundunar ‘yan sanda, DSP Mohammed Jalige, ya ce dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifinsu.

A cewarsa, ‘yan matan biyu da ke zama budurwar ‘yan fashin, sun kuma taimaka wa barayin da harkar makamai.

“Mai laifin da ake zargin ya kuma amsa laifin sa tare da wasu ‘yan kungiyar wajen gudanar da ayyuka a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Zariya da kuma makwabta, amma ana ci gaba da gudanar da bincike,” in ji PPRO.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN