Da dumi-dumi: Daruruwan mutane sun kone kurmus sakamakon bala'in gobara da ta tashi a wani babban gini a kasar Sin (Bidiyo)


Wata babbar gobara a ranar Juma'a, 16 ga watan Satumba, ta kone wani babban bene, rahotanni sun ce yana dauke da kamfanin sadarwa na China Telecom a birnin Changsha, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar Sin suka ruwaito, inda daruruwan mutane ake fargaban sun kone kurmus.

A cewar rahotanni, ba a san adadin wadanda suka mutu ba tukuna amma faifan bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna dumbin benaye da ke cin wuta da ke nuni da girman bala'in.

Tashar talabijin ta CCTV ta kasar Sin ta ruwaito cewa, " hayaki mai kauri yana ta fitowa daga wurin, kuma benaye dozin da dama na ci gaba da konewa."

Rahotannin cikin gida na nuni da cewa an kwashe mutanen daga ginin mai tsayin kimanin mita 200. China Telecom babban aiki ne na gwamnati wanda ke daukar dubban daruruwan ma'aikata. Ba a san ko nawa ne ke aiki a hasumiya ta Changsha ba kuma kafofin yada labaran kasar sun ce ba a kai ga tantance adadin wadanda suka mutu ba.

Kamar dai yadda aka saba, an kashe gobarar amma wani gefen ginin ya kone gaba daya, yayin da hayaki mai kauri ke ci gaba da ruruwa a iska.

Changsha babban birnin lardin Hunan ne na kasar Sin, inda kimanin mutane miliyan 10 ke zaune.

Kalli bidiyo a kasa...

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN