Bayan rawa da zagi a kan kabarin wata tsohuwa, Kotu ta yanke wa saurayi hukuncin bulala 40 da daurin watanni 27 a Kurkuku


Wata Kotu da ke zamanta a Unguwar Gama a Jihar Kano ta yanke wa wani Abdullahi Umar hukuncin bulala 40 da daurin watanni 27 a gidan yari bisa samunsa da laifin zagin wata matacciya. 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama Abdullahi a watan da ya gabata bayan wani faifan bidiyo na TikTok da ya nuna yana zagi da rawa a kan kabarin mahaifiyar abokinsa da ta rasu.

A cikin faifan bidiyon, an ga Abdullahi yana tsaye saman wani kabari yana zagin mamaciyar da aka binne a cikinsa.

“Wannan kabarin Mahaifiyar Mai Abun Duniya ke nan,” in ji shi a lokacin da yake nuna kabarinta, “Kuma kamar yadda danta ya zo gidanmu ya ci zarafin mahaifiyata, ni ma ina nan ne domin in ci zarafin iyayensa,” in ji shi.

An kuma ji shi a cikin faifan bidiyon yana kalubalantar abokin hamayyarsa da ya same shi a makabarta ya daidaita maki tsakanin su. 

Har yanzu ana kan zayyana cikakkun bayanai a lokacin gabatar da wannan rahoto amma an tattaro cewa an yanke masa hukunci a ranar Juma’a, 16 ga Satumba, 2022. 

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN