Gwamna Atiku Bagudu ya shiga tsakani a rikicin da ya barke tsakanin yan acaba da jami’an hukumar FRSC a Birnin kebbi

Gwamna Atiku Bagudu ya shiga tsakani a rikicin da ya barke tsakanin masu tuka babura da jami’an hukumar FRSC a Birnin kebbi


Gwamna Atiku Bagudu na Kebbi ya shiga tsakani a rikicin da ya barke tsakanin masu tuka babura da jami’an hukumar FRSC, lamarin da ya kai ga toshe hanyoyin mota a Birnin Kebbi.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa a ranar Juma’ar da ta gabata ne masu tuka baburan ‘yan kasuwan suka tare tituna a babban birnin jihar domin nuna rashin amincewarsu da kamasu ba bisa ka’ida ba da kuma kwace musu baburan da jami’an tsaro suka yi a kai a kai.

Sai da Gwamnan ya shiga tsakani kafin masu tuka babura su kaurace wa titunan domin ba da damar zirga-zirgar ababen hawa.

Ya yi alkawarin gudanar da bincike kan lamarin tare da nemo mafita mai dorewa kan matsalar da ta dade.

Bagudu ya umurci hukumomin Gwamnati da abin ya shafa da su tattauna da kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) da kuma kwamishinan ‘yan sanda domin ganin an shawo kan lamarin.

Gwamnan, ya ce duk da cewa masu tuka babur din na da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin jihar, amma dole ne su koyi tattaunawa a maimakon yin ayyukan da ba su dace ba.

Bagudu, ya ce Gwamnati ba za ta hana zirga-zirgar babura na kasuwanci ba kamar yadda ake yi a wasu jihohi, ya kuma gargade su da su rika bin ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa.

Gwamnan ya bayar da gudummawar Naira miliyan daya ga masu tuka baburan domin jin dadin rayuwarsu.

Mai ba Gwamna shawara na musamman kan harkokin wutar lantarki, Alhaji Yusuf Haruna-Rasheed, ya shawarce su da su rika kai kokensu ta hanyar shugabancin kungiyar tasu, domin sasantawa.

Tun da farko shugaban kungiyar masu sana'ar babura na jihar, Malam Nafi'u Zakari, ya shaidawa Gwamnan cewa zanga-zangar ta biyo bayan kamasu da kuma kwace musu babura da hukumar FRSC ta yi ba tare da karya wata doka ba.

Ya kuma yabawa Gwamnan kan yadda ya taka rawar uba a lamarin

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN