Madalla: Bagudu yayi alkawarin magance wata babbar matsala ga al'umma

Bagudu yayi alkawarin magance wata babbar matsalar ga al'umma


A ranar Asabar din da ta gabata ne Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya baiwa mazauna garin Dutsin Fakara dake karamar hukumar Arewa tabbacin samar da ruwan sha. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa gwamnan da ke kan hanyarsa ta zuwa garin Bachaka a karamar hukumar, ya hangi wasu gungun mata da ke kokarin diban ruwa a wata rijiya da ta ja hankalinsa.

Bayan da ya yi tambayoyi game da matsalar ruwa daga matan, ya yi alkawarin samar da rijiyar burtsatse don samar da ruwan sha ga al’umma.

A cewarsa, hakan na daga cikin kokarin gwamnatinsa na samar da ababen more rayuwa ga al’ummar jihar musamman mazauna karkara.

Mazauna yankin sun nuna matukar farin ciki da godiya ga gwamnan bisa yadda ya nuna kulawa.

A garin Bachaka dake kan iyaka a karamar hukumar Arewa, Gwamnan ya duba wani gini da ya ruguje sakamakon zaizayar kasa a wata makarantar firamare ta Model.

Tun da farko, Gwamnan ya duba aikin gina titunan garin Gulma da ke karamar hukumar Argungu da kuma zaizayar kasa a Dukku da ke karamar hukumar Birnin Kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN