Gwamna ya gaggauta rufe otal bayan an gudanar da pati na aikata lalata karara kuma aka yada bidiyon lamarin

Gwamna ya gaggauta rufe otal bayan an gudanar da pati na aikata lalata karara kuma aka yada bidiyon lamarin 


Kungiyar kare hakkin jama’a (CLO) ta yabawa Gwamna Charles Soludo na Anambra bisa gaggaucewar matakin da ya dauka na rufe otal din Winters Garden saboda wani hoton bidiyo na lalata da aka gudanar a otal din.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar ta CLO, Mista Vincent Ezekwueme ya sanya wa hannu kuma aka bai wa manema labarai a Onitsha ranar Asabar.

Kungiyar ta CLO ta jinjinawa Gwamna Soludo bisa namijin kokarin da yake yi wajen ganin an samar da kyawawan dabi’u a gwamnatinsa da jiharsa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Soludo ya rufe otal din Winters Garden da Suites a Awka, babban birnin jihar, a kan wani hoton bidiyo na jima'i da aka ce an yi a wani sashe na otal din.

A cewar sanarwar, abin takaici ne yadda irin haka ta faru a cikin al’umma duk da yajin aikin da malaman jami’o’in suke yi na tsawon watanni shida, wanda ya tilasta wa dalibai yin hutun da ba a shirya ba.

“Akwai bukatar a kai ga tushen da kuma tabbatar da hakikanin masu tallata shaitan da shirya taron shaidan; ’Yan Najeriya na da kwarin guiwa da neman sanin wadanda suka shirya shi da kuma dalilinsa.

"Abin takaici ne kuma abin ƙyama ne cewa wannan abin ban dariya da rashin kunya ya haifar da mummunan zato da tasiri ga jihar da 'yan ƙasa," in ji shi.

Ezekwueme ya bayyana lamarin a matsayin abin kunya, mai raÉ—aÉ—i da ban tsoro da kuma illa ga matasa, al'umma da kuma jihar

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN