Siyasar Kebbi: Faruku Madawakin Bunza ya yi fashin baki, ya bayar da satar amsa ga yan siyasar Kebbi ta tsakiya gabanin zabukan 2023, duba ka gani


Wani matashi kuma fitaccen dan siyasa a garin Bunza na jihar Kebbi Alhaji Faruku Madawakin Bunza, ya yi fashin baki dangane da alkiblar siyasar Kebbi ta tsakiya musamman yankin Bunza gabanin zaben 2023. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

Alhaji Faruku ya ce:

"Yakamata Yan takara su yi tunani da manyan Yan siyasa. Manya da masu mukamai Yan kwangiloli da Yan siyasa wanda an dasa su shin me sukayi wa jama'a wanda zai sa jama'a su biyo su. Idan har sun yi wa jama'arsu amfani, to su koma can wajen jama'arsu domin su nemi jama'a". 

"Akwai  wadanda basu kulla wa mutane komi ba, kai kana Dan siyasa ko an yi maka mukamin Gwamnati don ka taimaki mutane, baka yi wa kowa komi ba. Mutane basu san amfaninka ba, Mazabarka (Ward) dinka basu San amfaninka ba, karamar hukumar ka basu san amfaninka ba. Ta yaya za ka fito gobe ka fada wa mutane magana su yarda da kai?".

"Ire-iren wadannan ya kama Yan siyasa su sani domin su san irin wadanda ya kamata su yi tafiya da su. Ba irin mutanen da za su danfare su ba su ce suna da mutane alhalin ba su da su. Idan kana da mutane ka koma Mazabarka a san kana da mutane, wannan shi ne siyasa, ba wai a koma ana amfani da Bakauye ba ana zaluntarshi".

"Ba wai maganar ka karbi kudi daga wajen Dan siyasa ba, amma ka je ga jama'arka ka nema masa mutane a Mazabarka, a san kana da mutane ka nemesu a kai ga nassara, wannan ba zai manta da kai ba.

"Zancen masu cewa an bamu kudi ne, tun lokacin da aka fara waccan siyasa, Alhaji Abba Aliero da Faruku Enabo suka zo gidan marigayi Abba dogo aka ce mu kulla amana, tun wannan lokaci duk wanda ke garin Bunza da kewayen jihar Kebbi ya gan gudunmuwar da na yi a gidana da shaguna na". 

"Tun daga wannan lokacin har zuwa yanzu, ba wanda ya taba bani Naira dubu hamsin N50.000 a jihar Kebbi, idan akwai shi ya fito ya karyata. Ina siyasa ne ra'ayi na, wanda ya san ni ya san akida ta. Amma babu dan takara ko Sanata ko Gwamna ko Dan Majalisa da ya taba bani dubu hamsin a Kebbi idan akwai ya karyata. 

"Siyasa ra'aiyina ce mun kulla alkawurra da wadanda muka kulla, sun sani. Muna son mutane su sani cewa muna siyasa ne don ra'ayinmu ba kudi aka bamu ba". Inji Alhaji Faruku. 

Latsa nan ka kalli bidiyo:

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN