2023: Wasu 'Yan BS sun tuba sun mika makamai, sun shiga wata jamiyar siyasa, sun bayyana wadanda ke daukar nauyinsu a jihar Arewa


2023: Wasu 'Yan BS sun tuba sun mika makamai, sun shiga wata jamiyar siyasa, sun bayyana wadanda ke daukar nauyinsu a jihar Arewa

Wasu ‘yan bangar siyasa a Zamfara sun yanke shawarar yin sabon salon rayuwa, su rungumi zaman lafiya, tare da bayar da kansu don yin amfani da Gwamnatin jihar don yin tasiri ga al’umma.

Baba Karami da Garba Lawal ne suka jagoranci ‘yan bangar siyasa a ranar Litinin, 5 ga watan Satumba, sun ce sun yi nadamar yadda wasu ‘yan siyasa ke amfani da su wajen kaddamar da ta’addanci a kan ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba, inji rahoton Daily Nigerian.

Da suka koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Yan bangan siyasar sun yi alkawarin taimakawa gwamnati a kokarinta na yaki da rashin tsaro a jihar.

Dukansu Karami da Lawal sun bayyana cewa tuban nasu ya biyo bayan fahimtar da suke yi cewa yayin da suke bata rayuwarsu ta hanyar kare muradun wasu ‘yan siyasa, ‘ya’yan irin wadannan ’yan siyasar suna makarantu masu kyau da kuma hawa mataki na sama a rayuwa.

Shugaban karamar hukumar ya karbi bakuncin ‘yan bangar siyasar a Zamfara

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC a Zamfara, Yusuf Idris, ya ce ‘ya’yan kungiyoyin sun mika makamansu ne domin nuna aniyarsu ta yi wa gwamnatin jihar aiki.

A nasa bangaren, Babangida Abdullahi, tsohon shugaban karamar hukumar Gusau, ya karbi kungiyoyin da makamansu, ya kuma yi alkawarin mika harsashin ga jami’an tsaro.

Abdullahi ya yaba musu bisa yadda suka rungumi zaman lafiya tare da yin alkawarin bayar da gudumawa wajen ci gaban Zamfara.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN