An cafke shahararren mai sayar da makamai ga ‘yan bindiga a jihohin Katsina, Kaduna da Neja


Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Neja sun cafke wani kasurgumin dillalin makamai da kuma kai wa ‘yan fashi, Umar Shehu. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Kakakin rundunar, DSP Wasiu Abiodun, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata, 6 ga watan Satumba, ya ce an kama wanda ake zargin ne a karamar hukumar Gurara ta jihar.

Wanda ake zargin ya amsa laifin bayar da makamai da alburusai ga ‘yan bindiga a dazuzzukan Neja, Katsina da Kaduna. 

“A ranar 20/08/2022 da misalin karfe 5 na yamma, rundunar ‘yan sandan da ke a mahadar Dikko tare da hadin gwiwar ‘yan kungiyar FIB, sun kama wani Umar Shehu mai shekaru 31 ‘m’ Bakori, karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina. sanarwar ta karanta. 

“An kama wanda ake zargin ne a Junction Dikko, karamar hukumar Gurara bisa samun sahihan bayanan sirri, bayan da aka gano shi tare da zarginsa a matsayin wani katafaren dillalin makamai da ke kaiwa sansanonin ‘yan bindiga daban-daban a Katsina, Kaduna da Jihar Neja.

“Lokacin da ake yi masa tambayoyi, ya amsa cewa ya bayar da makamai da harsasai ga ‘yan bindiga a dajin Madaki Katsina, sansanin Ganai da ke dajin Maidaro Kaduna da kuma wani dan kungiyar da ke addabar yankin Kwamba/Maje a Suleja.

“Ya kara da ikirarin cewa ya siyo makamai daga hannun Abdulmani ‘m’ na jihar Taraba wanda hukumar FIB ta kashe a farkon wannan shekarar, ya ce ya samu naira dubu dari a duk alburusai 500 da ya kai sansanin ‘yan fashi." 

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN