Wani Jariri, mata 4 sun mutu a hatsarin Kwalekwale a jihar Jihawa, duba yadda ta faru

Jariri, mata 4 sun mutu a hatsarin kwalekwalen Jigawa – ‘Yan sanda


Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wani jariri dan wata bakwai da mata hudu a wani hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Guri.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) a jihar, DSP Lawan Shiisu, ya tabbatar da faruwar lamarin a Dutse ranar Laraba.

“A ranar Talata da misalin karfe 6 na yamma, bayanai da muka samu sun nuna cewa a ranar da misalin karfe 4:30 na yamma wasu mata hudu da wani yaro suka shiga kwale-kwale daga Nguru Yobe zuwa kauyen Adiyani da ke karamar hukumar Guri ta jihar Jigawa.

“Abin takaici, kwalekwalen ya kife kusa da inda suke. Direban ya yi nasarar tserewa da ransa, yayin da fasinjan suka nutse a ruwa,” in ji Shiisu.

Ya ce nan take masu nutsewa a yankin suka yunkuro domin ceto fasinjojin, inda suka samo gawarwakin.

Hukumar ta bakin PPRO ta ce an kai gawarwakin zuwa asibitin Adiyani kuma Likitan ya tabbatar da mutuwar su.

Shiisu ya bayyana sunayen wadanda suka mutun a matsayin Oneyaniwura Kasagama mai shekaru 50 da Lafiya Bulama mai shekaru 40 da Badejaka Kasagama mai shekaru 40 da Gimto Kasagama mai shekaru 40 da Mai Madu Bulama jariri dan watanni bakwai.

PPRO ya ce wadanda abin ya shafa dukkansu mazauna kauyen Adiyani ne, ya kara da cewa

An fara bincike kan lamarin

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN