Yanzu-yanzu: Wani mutum ya yi kokarin tserewa daga Kotu bayan yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin fyade da kashe wata budurwa (Bidiyo-Hotuna)


An yada hoton bidiyon wanda aka samu da laifin fyade kuma mai kisan kai, Uduak Akpan, yana kokarin tserewa daga babbar Kotu bayan yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya. Shafin la arai na Isyaku News Online (isyaku.com) ya samo.

Mai shari’a Bassey Nkanang na babbar kotun jihar Akwa Ibom ne ya yanke wa Uduak hukunci a yau 4 ga watan Agusta, bisa laifin aikata fyade da kashe Iniubong Umoren

Umoren, wanda ta kammala karatun Falsafa, Jami’ar Uyo, an kashe ta ne a watan Afrilun 2021. Marigayiyar tana neman aiki ne a lokacin da take jiran daukar nauyin shirin yi wa kasa hidima na tilas (NYSC) a lokacin da ta ci karo da Akpan wanda ya ce yana da aiki da zai dauke ta. Da isa gidansa, Akpan ya yi mata fyade, sannan ya kashe ta.

Jim kadan bayan yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya, Uduak ya yi yunkurin tserewa daga dakin Kotun.Kalli hotuna da bidiyonsa bayan an kama shi a kasa...

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN