FYADE: Wani mutum dan shekara 50 ya yi wa wata Marainiya mai shekaru 7 fyade da rana kiri-kiri


Danladi Daniel, dan shekara 50, ma'aikacin  kwalejin ilimi ta Akwanga, a karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa, an kama shi bisa zargin laifin lalata da wata yarinya marainiya mai shekaru bakwai. Shafin labarai na Isyaku News Online (isyaku.com) ya samo.

Rahotanni sun bayyana cewa yarinyar tana zaune tare da Kakanta tsawon shekaru hudu a Ungwar Loko da ke kauyen Gwanje a karamar hukumar Akwanga a jihar Nassarawa, bayan iyayenta sun rasu.

Da take ba da labarin irin halin da ta shiga, yarinyar ta bayyana cewa, wata rana ta tashi daga barci sai ta gano cewa ita kadai ce a gida; don haka ta yanke shawarar zama a wajen harabar gidansu su.

Ta bayyana cewa wani ‘Uncle Dan’ wanda gidansu ke kusa da nasu ya nemi ta zo ta same shi, amma ta ki. 

Ta ce; 

“Ya tafi, sai ya dawo yana yin kamar zai debo ruwa a rijiyar. Kuma kafin in san me ke faruwa sai ya ja ni zuwa dakinsa ya cire wandona ya kwana da ni”.

Kakan wanda abin ya shafa ya tuna bai ga jikarsa a gida ba a ranar da lamarin ya faru. 

Yace; 

 “Imanina da farko shi ne cewa an yi garkuwa da jikata zuwa wani wuri da ban sani ba. Gaba daya na rude da bacin rai lokacin da ban gan yarinyar ba.

“Lokacin nemanta a cikin unguwar ina ci gaba da kiran sunanta a cikin tsawa, sai na ga ta fito daga dakin Dan da alamar gajiya a jikinta, Idanuwanta sunyi jajawur; gumi take yi.

“Na tambaye ta me ya faru, sai ta bayyana cewa makwabcina, Danladi Daniel ya ja ta zuwa dakinsa ya yi lalata da ita. Nan take na kai ta wata cibiyar lafiya da ke kusa don a gwada ta, aka tabbatar da cewa an yi lalata da ita. Mun kuma ga jini a tufafinta da al’aurarta.”

A daya bangaren kuma jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel ya ce an kama wanda ake zargin.

Nansel ya ce; 

“An kama wanda ake zargin, Mista Danladi Daniel, wanda ba malami ne a kwalejin ilimi ta Akwanga ba, da laifin lalata da Marainiya mai shekaru bakwai da haihuwa.” 

Tuni dai aka mika wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka da ke Lafiya domin ci gaba da bincike.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN