Yanzu yanzu: Yan sandan jihar Kebbi sun cafke wata matar aure bisa zargin kashe mijinta da wuka a Aliero kwatas Gwadangaji jihar Kebbi


A ranar 25/8/2022 da misalin karfe 9:40 na dare ‘yan sandan da ke hedikwatar ‘yan sanda reshen Gwadangaji suka samu labarin cewa, an ji wata hayaniya da ake zargin wani bakon abu ne daga gidan wani makwabci mai suna Attahiru Ibrahim da ke unguwar Alieru Quarters a Birnin Kebbi a jihar Kebbi, amma kofarsa a kulle. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Sanarwar haka na kunshe ne a wata takarda da Kakakin rundunar Yan sandan jihar Kebbi SP. Nafi'u Abubakar ya raba wa manema labarai da safiyar Juma'a a garin Birnin kebbi. 

Ya ce bayan samun labarin, Yan sanda sun garzaya da tawagar ‘yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka tilastawa kansu kutsawa cikin gidan sabida sun tarar da kofar gidan a rufe, shigarsu gidan ne suka tarar da Attahiru Ibrahim a kwance a cikin jininsa, daga bisani Likitan lafiya ya tabbatar da mutuwarsa. Hakazalika, an ga matar sa daya, Farida Abubakar mai shekaru 30 a cikin gidan. Don haka, an zarge ta kuma aka kama ta a kan lamarin.

Don haka kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi CP Ahmed Magaji Kontagora ya umurci DPO da ya gaggauta mika karar zuwa SCID da ke Birnin Kebbi domin gudanar da bincike na gaskiya da zummar bankado yadda lamarin ya faru.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN