Kamfanin Kebbi Home Saving and Loan Limited ya kafa kwamitin karbar lamuni domin karbo lamuni daga abokan huldar sa. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa Mukaddashin Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Bankin, Alhaji Abdullahi Sa’idu ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi ranar Alhamis.
Ya ce wani bangare na aikin kwamitin shi ne dawo da basussukan da aka rabawa wadanda suka amfana daban-daban, inda ya ce kwamitin zai kasance karkashin sa.
Ya bukaci kwastomomin da su tabbatar sun biya bashin, ya kara da cewa, “su fahimci cewa duk da cewa cibiyar banki ce ta Gwamnati da kuma cibiyar hada-hadar kudi, ba ta da wani bambanci da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi.
“Hukumar da ke kula da cibiyoyin hada-hadar kudi a Najeriya ce ke kula da cibiyar kuma a lokaci guda dukkanmu muna aiki a kasuwa daya.”
Manajan ya kara da bayyana karancin kudade a matsayin lamari da ke fuskantar ci gaban ayyukan bankin.