Yan bindiga sun tilasta wa mazauna kauyuka 8 tserewa daga kauyukansu a jihar Kebbi


A kalla kauyuka takwas ne a karamar hukumar Augie ta jihar Kebbi suka zama ba kowa saboda hare-haren da ‘yan bindiga suka kai musu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.

Shafin isyaku.com ya samo cewa NAN ta ambato Kauyukan da lamarin ya shafa wanda suka hada da Zagi, Tungar Rafi, Tungar Tudu, Keke, Kwaido, Sabongarin Kwaido, Tungar Chichira da Tattazai.

Mazauna kauyukan sun yi kaura ne da yawa bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari Zagi a daren Laraba.

Harin dai an ce ya yi sanadin mutuwar mutane uku, da dama sun jikkata, sannan wasu 15 an yi awon gaba da su.

Hakimin kauyen na Zagi, Malam Muhammadu Lawali-Sule ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne da tsakar dare.

Ya ce mutanen kauyen baki daya sun fuskanci maharan amma ‘yan bindigar suka ci karfinsu.

Shugaban kauyen ya ce wadanda suka jikkata a harin na kwance a asibiti kuma suna karbar magani.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Alhaji Ahmed Magaji-Kontagora, ya ce an tattara karin jami’an tsaro zuwa yankin domin tallafa wa wadanda ke kasa.

Ya kuma tabbatar da cewa sojoji sun tare ‘yan bindigar tare da hana su shiga ko’ina.

Magaji-Kontagora ya shawarci mutanen da suka gudu da su koma garuruwansu su ci gaba da sana’o’insu na yau da kullum.

Ya bada tabbacin cewa za a kare rayukansu da dukiyoyinsu.

Kwamishinan ‘yan sandan ya yi kira ga jama’a da su kasance masu taka-tsan-tsan da kuma kula da harkokin tsaro, tare da tallafa wa jami’an tsaro da sahihancin bayanai wajen bayar da taimako domin magance tashe-tashen hankula.

Da aka tuntubi shugaban karamar hukumar Augie, Alhaji Lawal Muhammad ta wayar tarho, ya ce an tsaurara matakan tsaro a kewayen kauyukan da sauran yankunan.

Ya kara da cewa an kafa sansanin ‘yan gudun hijira a yankin.

“Dole ne mu yaba wa jami’an tsaro a jihar kan yadda suka tura jami’an tsaro domin dakile sake afkuwar lamarin.

“Ba tare da bata lokaci ba jami’an tsaro sun mayar da martani ta hanyar tura karin jami’ai, kuma yanzu haka al’amura sun dawo yankin.

“Ina so in yi kira ga mutanen da suka bar al’ummarsu da su kasance masu hakuri da natsuwa.

“An kafa sansanin ‘yan gudun hijira a wata Makaranta da ke yankin.

“Gwamnati da hukumomin tsaro suna iyakacin kokarinsu domin sun san halin da suke ciki kuma za su yi duk mai yiwuwa na dan Adam wajen kare rayukansu da dukiyoyinsu,” in ji shugaban.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN