Duba abin da zai faru da farashin man fetur bayan Ministan Buhari ta bayyana lokacin da za a cire tallafin a ƙarshe


Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed, ta ce za a cire kudaden tallafin da ake kashewa kan man fetur a tsakiyar shekarar 2023.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Ministan ta bayyana haka ne a gaban Kwamitin wucin gadi na Majalisar wakilai da ke binciken tsarin tallafin tsakanin shekarar 2013 zuwa 2022 a ranar Alhamis 18 ga watan Agusta.

Zainab, a yayin gabatar da jawabinta, ta bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta gabatar da wata sabuwar ranar da za ta kawo karshen tsarin tallafin, inda ta bayyana cewa tallafin ba zai dore ba, kuma zai iya ingiza Gwamnatin ta kara bashi a 2023.

Ta kara da cewa Gwamnati ta shirya biyan tallafin ne na rabin shekara mai zuwa, inda ta bada misali da tsarin kashe kudi na matsakaicin zango na 2023-2025 da kuma takardar dabarun kasafin kudi.

A cewarta, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon MTEF/FSP ga shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan da Kakakin Majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila kamar yadda Majalisar tattalin arzikin kasa da Majalisar zartarwa ta tarayya suka amince da ita.

Ta bayyana cewa, “Abu daya da ya yi fice a tsarin kashe kudi na matsakaicin zango shi ne, idan har al’ummar kasar nan za su ci gaba da bayar da tallafin mai kamar yadda aka tsara a yanzu, za a rika biyan mu daga watan Janairu zuwa Disamba, kudin tallafi na N6.4tn.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN