An kai hari kan ayarin motocin matar Gwamnan Osun, yan sanda sun kama mutane 5 da ake zargi


Rundunar ‘yan sandan jihar Osun, a ranar Asabar ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun kai wa ayarin motocin Misis Kafayat Oyetola, matar Gwamnan Osun hari ranar Juma’a a Owode da ke Ede. Shafin isyaku.com ya samo.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ta ruwaito cewa a wata sanarwa da Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, SP Yemisi Opalola ya fitar, jami’an tsaro daya a cikin ayarin ya jikkata.

Ya kara da cewa ‘yan sanda sun kama mutane biyar da ake zargi da kai harin.

“A ranar Juma’a, da misalin karfe 8:30 na dare, ‘yan sanda sun samu sahihin bayani cewa, a Owode, babbar titin Kasuwar Ede, wasu ‘yan bindiga sun far wa ayarin motocin matar Gwamnan Osun.

“Ba tare da bata lokaci ba jami’in ‘yan sanda na ‘A’ Dibision, Ede, ya tattara tare da jagoranci jami’an bincike zuwa wurin da lamarin ya faru, inda rundunar ta hadu da CSP Dauda Ismail, babban jami’in tsaro na Gwamna Gboyega Oyetola na Osun.

“CSP Ismail ya bayyana wa tawagar cewa wani Omolola Opeyemi, direban Ijebu-Ode, jihar Ogun, ya tuka wata babbar mota da ba ta da rajista sannan ya tare hanyar Oyetola.

“Sakamakon kulle-kullen da aka yi, wasu ‘yan iska sun yi amfani da damara suka fara jifan ayarin motocin matar Gwamnan, inda suka raunata direban babbar motar a goshinsa, tare da raunata wani jami’in DSS.

“Duk da haka, an kama mutane biyar daga wurin kuma ana ci gaba da bincike.

"Za a sanar da ƙarin ci gaba daga baya." Opalola ya ce.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN