Yan bindiga sun sake kai farmaki cikin birnin Katsina, mutane sun tarwatse


Mazauna Sabon Gida, Anguwar Makudawa, Anguwar Shola Quaters da Asibitin koyarwa na tarayya (FTH) da Anguwar ma'aikatan Katsina sun yi gudun neman tsira yayin da yan bindiga suka shiga yankin da tsakar rana.

A rahoton Daily Trust, wani shaida, wanda ya yi ikirarin ya ga zuwan yan bindigan da karfe 1:30 na rana, ya ce yan ta'addan sun biyo wasu makiyaya ne lokacin da suka shiga Anguwar Sabon Gida.

Shaidan ya ce:

"Makiyayan na tsaka da kiwo a kewayen Lambun Malam Mu'azu, ba zato suka ga yan bindigan, nan take suka fara gudu da dabbobin su zuwa yankin Sabon Gida, hakan ya sa mutane suka fara gudun tsira."

Wani mazaunin FTH ya ce mafi yawan mutane sun kwashe iyalansu daga yankin sabida tsoron harin yan bindiga, ganin cewa, "Idan yan ta'adda zasu iya zuwa da rana, Allah kaÉ—ai yasan abinda zai faru da daddare."

Shin dagaske FTH sun É—auki mataki?

Yayin da aka tuntuɓe shi kan raɗe-raɗin dake yawo cewa an umarci mutane su bar Asibitin FTH, Kakakin Asibitin, Bishir Muhammad, ya ce ba bu wani abu kamar haka daga ofishin Daraktan FTH.

Sai dai ya tabbatar mutane sun shiga tashin hankali a yankin, inda ya ce:

"Mutane sun tsorata, dagaske sun ga yan fashin daji daga nan hankalin su ya tashi kuma idan kaga mutane na tattara kaya zasu tafi, ba zaka hana su ba. Amma maganar gaskiya ba wanda ya umarci su bar yankin."

Wane mataki hukumomi suka É—auka?

Mataimakin kwamandan Wakilin Yamma 1, wata ƙungiyar Yan Banga da ke yankin, Abdullahi Usman Ɗan Daura, ya ce duk da barazanar gaskiya ne amma yadda mutane suke zuzuta abun ya ƙara dagula lamarin.

"Muna aiki tare da haÉ—in guiwar hukumomin tsaro kuma muna iya bakin kokarin mu, amma babban kalubalen na tattare da Imfoma waÉ—an da ke faÉ—a wa yan ta'addan mutanen da zasu sace da kuma inda jami'an tsaro suke."

Jam'iyyar APC a jihar Oyo ta yi gargaÉ—in cewa tsaron jihar na cikin matsala idan har gwamna Makinde ya zarce a Ofis a 2023.

A wata sanarwa, APC mai adawa a jihar ta ce daga zuwan Makinde ya lalata duk wani tubalin zaman lafiya da tsohon gwamna ya gina.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN