APC za ta fara yakin neman zaben shugaban kasa a ranar 28 ga Satumba, duba yadda tsarin yake


Bayan wasu sauye sauyen tsare-tsare, jam’iyyar APC ta bayyana shirin fara gangamin yakin neman zaben shugaban kasa a ranar 28 ga watan Satumba.

A yau ne aka shirya gudanar da taron kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na APC karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu, domin yanke shawara kan ranar da kuma shirya taron kwamitin zartarwa (NEC) na jam’iyyar APC na kasa.

Bincike ya nuna cewa a taron karshe da NEC ta APC ta gudanar a watan Afrilu, ta mika ragamar mulki ga kwamitin ta na NWC na tsawon kwanaki 90, Tribune Online ta ruwaito.

Wata majiyar jam’iyyar ta bayyana cewa taron na gaggawa da NEC za ta yi ya zama dole ne domin wancan kwamitin ya sabunta ikonsa da aka mika wa NWC karkashin jagorancin Sanata Adamu.

Bayan cikar kwanaki 90 din, wata majiya mai karfi ta shaida wa jaridar This day cewa, NWC ba za ta iya daukar muhimman shawarwari a madadin jam’iyyar ba ba tare da amincewar kwamitn na NEC ba.

Majiyar ta ce:

“Yayin da wa’adin watanni uku ya kare tun daga ranar 22 ga watan Yuli, NWC ba za ta iya daukar muhimman shawarwari a madadin jam’iyyar ba ba tare da amincewar NEC na, kuma bisa la’akari da yadda tsarin mulki ya tanada, wasu mambobin NWC na kokarin ganin an yi taron gaggawa na NEC."

Kamar yadda kudurorin taron NEC na watan Afrilu ya tanada kuma sakataren yada labaran jam’iyyar APC na kasa, Felix Morka, ya karanta wa manema labarai, ya bayyana cewa, an mika ikon NEC mai lamba 13(3)(ii)(iii) (iv)(v) da (vi) ga NWC na tsawon kwanaki 90.

Don haka ne aka bai NEC ikon sauke ayyukan hukumar kamar yadda yake a shafi na 13.3 (ii) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN