Da dumi-dumi: Lantarki ya kashe wani saurayi da ya shiga transfoma don yin sata.. Isyaku News


Wutan lantarki ya kashe wani mutum da ake zargin barawo ne a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa. Shafin Isyaku News Online isyaku.com ya samo.

Rahotanni sun bayyana cewa wanda abin ya shafa ya je yin sata a na’urar taranfoma ne kwatsam aka dawo da wuta.

Mazauna yankin sun tashi ne da safiyar Laraba, 10 ga watan Agusta, inda suka ga gawar mamacin kwance a cikin magudanar ruwa.

"Yau mun tashi ne muka ga gawar wani matashi a kan taransfoma a kusa da titin Osiri, ya yi nasarar yanke biyu daga cikin Wayoyin wutan amma ba zato ba tsammani ya gamu da ajalinsa sakamakon mayar da wutar lantarki yayin da yake cikin satar wayar." wata majiya ta ce.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN