Wasu ma'aurata, Muhammad Umar da matarsa Sayyada Shamsiyya, sun rasu a jihar Katsina.
Har yanzu babu cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru, amma an tattaro cewa ma’auratan da suka yi aure a bara, an tsinci gawarsu a gidansu da ke Unguwar Rahamawa a cikin birnin Katsina da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Juma’a 19 ga watan Agusta, 2022.
Makwabtan sun bayyana cewa ma’auratan ba su nuna alamun rashin lafiya ba, inda suka ce sun halarci Sallar Juma’a kafin a same su a mace.
An yi jana’izar ma’auratan ne a safiyar ranar Asabar 20 ga watan Agusta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.