Kasar Mali za ta haramta yin Luwadi a hukumance ta hanyar samar da dokar haramci da hukunci kan Luwadi a fadin kasar. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Kafin yanzu dai babu wata tsayayyar doka da ta haramta yin Luwadi a kasar ta Afrika ta yamma.
Sai dai Ministan sharia na kasar Mali, Mahamadou Kassogue ya shaida wa manema labarai cewa zasu samar da doka kan haramta luwadi a kasar Mali .