Wata yar Duniya ta cije kunnen wani mutum har ya gundule kuma ta hadiye a gabansa


Wata Karuwa ta cije kunnen wani mutum a sashen kunnensa na dama kuma ta hadiye a gabansa a kasar Thailand.

Kannika Kamton, mai shekaru 25, an ce ta tuntubi dan yawon bude ido mai shekaru 55 bayan da ya hau wata motar buda ta baya a Thailand yayin da ya ke "cikin maye".

Ta shiga motar ne bayan ta tsaya a kan fitilar ababen hawa a Pattaya kafin ta kai hari kan mai yawon bude ido da ke cikin motar.

Ana zargin Karuwar ta nutse haĆ™oranta a cikin kunnuwan mutumin na dama yayin da jama'a  ke kallo cikin firgici a daren Asabar, 20 ga watan Agusta.

Yayin da wanda ta cije wa kunner ya yi kururuwa cikin azaba, Kamton ta hadiye guntun naman kunnen.

Kamton ta yi kokarin guduwa kafin a kira ‘yan sanda, amma ‘yan sanda sun kama ta

Daga nan aka kai ta ofishin ’yan sandan da ke yankin domin ta amsa tambayoyi.

Jami’ai sun daure kunnen mai “jini da yawa” a gefen titi, kafin a kai shi asibiti domin neman kulawar gaggawa.

Laftanar ‘yan sandan kasar Saijai Kamchula ya tabbatar da faruwar lamarin.

"Za a gurfanar da matar da ake tsare da ita, akwai shaidu da dama kuma wanda aka cinye wa kune na son a tsare matar a gurfanar da ita a gaban kuliya."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN