Yadda wani mutum ya lakada wa matarsa mai ciki duka har lahira, duba dalili.. Isyaku NewsWata mata mai juna biyu mai suna Beatrice ta sha dukan tsiya a hannun mijinta wanda aka fi sani da MOB a unguwar Sapele da ke karamar hukumar Sapele a jihar Delta. Shafin labarai na Isyaku News Online (isyaku.com) ya samo.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa lamarin ya afku ne a yammacin ranar Juma’a 5 ga watan Agusta a kusa da wata cocin sabuwar zamani, Mountain of Fire and Miracle Ministries, dake kan sabuwar titin Awolowo Road Extension, a Sapele.

An tattaro cewa mutumin ya fara cin zarafin matarsa ​​ne bayan ya tambayi dalilin da ya sa ta bar gida zuwa coci ba tare da yin ayyukan gida da ya kamata ba da kuma shirya abincin dare.

Mutumin da ya kasa hakuri bai jira matarsa ​​mai dauke da juna biyu ta yi mata bayani ba, sai ya buge ta kuma ya yi mata bulala da dama, lamarin da ya sa ta fadi nan take.

An ce masu wucewa da ’yan cocin sun garzaya wurin domin ceto matar. An tabbatar da mutuwar ta ne bayan da aka garzaya da ita asibitin da ke Obule. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN