Yan Arewa sun shiga firgici a jihar Imo bayan yan IPOB sun kashe yan kasar Nijar 8 suka gundule kan 1 suka tafi, yan sanda sun magantu.. Isyaku News


Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan Arewa mazauna Owerri, babban birnin jihar Imo sun shiga cikin firgici sosai biyo bayan kashe wasu ‘yan kasar Nijar takwas da ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) suka yi.

A cewar Daily trust, harin ya faru ne a ranar Litinin, 1 ga watan Agusta, lokacin da maharan suka kai hari a wani gini da ke Orogwe, Owerri, wanda galibi Hausawa ‘yan ci-rani ne daga Najeriya da Jamhuriyar Nijar suka mamaye.

‘Yan Arewan sun ce an kai harin ne saboda kungiyar IPOB ta dauki dukkan mutanen da ke zaune a yankin ‘yan ci-rani ne daga Arewa, ba tare da sanin wadanda abin ya shafa ‘yan kasashen waje ne ba.

Sun ce sun shiga fargabar rayuwarsu sakamakon hare-haren da kungiyar IPOB da reshenta na tsaro, Eastern Security Network (ESN) ke kai musu.

Shaidar gani da ido yayi magana

Wani ganau mai suna Abubakar Muhammad ya ce tun da farko ‘yan bindigar sun ziyarci al’ummar Hausawa a Orogwe da yammacin ranar Litinin inda suka tattauna da Hausawa mazauna yankin.

Kalamansa:

“Lokacin da suka zo da maraice, ba su da makamai. Sun yi musayar kalamai da mutane; ba mu ma san 'yan bindiga ne ba.

“Amma cikin dare sai suka dawo suna harbin mutanenmu, nan take suka kashe mutum bakwai, mutane takwas kuma suka samu raunuka, wani karin mutum daya kuma ya mutu a asibiti, mun binne su washegari (Talata).”

Muhammad wanda ke sayar da Suya (gasashen naman sa) ya yi nuni da cewa yawancin mutanen da aka kashe abokan aikinsa ne da kuma masu fataucin shanu.

Ya kara da cewa a baya ‘yan bindigar sun harbe wasu matafiya ‘yan Arewa a ranar Lahadi 31 ga watan Yuli.

“Sun bude wa motar bas wuta ne a lokacin da suka fahimci cewa matafiya ne ‘yan Arewa; da dama sun samu raunuka yayin da mutum daya kuma ya rasa ransa. Bayan kwana guda sai suka zo su kawo mana hari a Orogwe. Yanzu muna rayuwa cikin tsoro,” inji shi.

Sarkin Hausawa na jihar Imo ya tabbatar da harin

Rahotanni sun bayyana cewa Sarkin Hausawa na jihar Imo, Alhaji Auwal Baba Suleiman ya tabbatar da cewa mutane takwas da aka kashe sun fito ne daga jamhuriyar Nijar kuma an sallami wasu shida da suka jikkata daga asibiti a ranar Laraba 3 ga watan Agusta.

Yace:

“An kai harin ne a gidan da akasari mutanen da suka mamaye wurin sun fito ne daga Jamhuriyar Nijar. Suna gudanar da harkokinsu a nan; wannan (harin) yana faruwa na ɗan lokaci. Muna son gwamnati ta dauki wasu matakai."

Sarkin ya kara da cewa ‘yan bindigar sun yanke kan daya daga cikin wadanda aka kashe sannan suka tafi da shi.

Rundunar ‘yan sandan Imo ta mayar da martani

A halin da ake ciku kuma, rundunar ‘yan sandan jihar Imo a ranar Laraba ta tabbatar da cewa ‘yan kungiyar ta IPOB sun kashe mutane bakwai.

Kakakin ‘yan sandan, CSP Mike Abattam, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce ‘yan bindigar “da ake zargin mambobin haramtacciyar kungiyar IPOB ne da kuma reshenta na ESN sun zo ne da wata bakar Lexus jeep da babura uku dauke da mutum biyu kowanne, inda suka harbe mutanen a cikin wani gini. a Orogwe, Owerri West LGA, Jihar Imo."

Ya ce ginin na wani Sir Chima Ogbuehi ne, mazaunin Legas.

Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa:

“Jami’an ‘yan sanda (DPO) cikin gaggawa ya tattara mutanensa tare da goyon bayan tawagar rundunar ‘yan sandan zuwa wurin, amma da isarsu, ‘yan bindigar sun tsere nan da nan, suka kwace motar kirar Toyota Sienna mai launin shudi da kuma tawagar rundunar ‘yan sandan. cikin gaggawa suka bi su yayin da DPO da mutanensa suka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Owerri, inda suka kwashe gawarwakin zuwa dakin ajiyar gawa.

“Abin takaici, jimillar mutane bakwai ne suka rasa rayukansu a harin, yayin da wasu shida suka samu raunuka, aka garzaya da su Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC), Owerri, Jihar Imo.

“Kwamishanan ‘yan sanda, Mohammed Ahmed Barde, ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan lamarin, inda ya yi alkawarin cewa rundunar za ta zage damtse wajen ganin an kama wadanda suka aikata wannan danyen aiki tare da fuskantar fushin doka. ”

Rundunar ‘yan sandan ta yi kira da a kwantar da hankula tare da yin kira ga mazauna yankin da su taimaka musu da sauran jami’an tsaro ta hanyar basu sahihan bayanai da kuma kai rahoton duk wani abu na sirri da aka gani a yankunansu ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN