Yadda mahaifi da dansa suka mutu bayan sun makale a cikin rijiya


Wani mahaifi mai shekaru 60, Malam Bala da dansa, Sunusi Bala, mai shekaru 35, sun rasu a wata rijiya da ke Sabon Garin Bauchi, a karamar hukumar Wudil ta jihar Kano, a lokacin da suke zubar da ruwa daga cikinta. Shafin labarai na Isyaku News Online isyaku.com ya samo.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar a ranar Laraba a Kano, ta ce lamarin ya faru ne da safiyar Talata.

Ya ce: “Mun samu kiran gaggawa daga ofishin kashe gobara ta Wudil da misalin karfe 11:30 na safe daga wani Isma’ila Idris cewa wasu mutane biyu sun makale a cikin rijiya.

“Nan take mun aika da tawagarmu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 11:33 na safe

“An kira wani uba da dansa domin su yasge wata rijiya, Kuma sun yi nassarar yashe Rijiyar"..

“Amma, dan ya koma cikin rijiyar ya share ta amma sai ya makale ya shake.

"Mahaifinsa ya bi shi don ceto shi, a lokacin da shi ma ya makale ya shake saboda rashin iskar oxygen a cikin rijiyar," in ji Abdullahi.

Ya ce duk da haka an fito da wadanda abin ya shafa daga rijiyar a sume kuma daga baya aka tabbatar da sun mutu.

Abdullahi ya ce an mika gawarwakinsu ga Insp Felix Gowok na ofishin ‘yan sanda model na Wudil.

Ya ce dalilin faruwar lamarin shi ne rashin iskar oxygen

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN