Yadda aka shake yarinya yar shekara 13 har Lahira bayan an yi mata cikin shege kuma aka kone gawarta a jihar Arewa


An sami gawar wata yarinya ‘yar shekara 13 da aka kashe kuma aka kone gawarta, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi SP Ahmed Wakil ya ce mahaifinta, Alhaji Danladi Mohammed na kauyen Mai’ari Arewa ne ya kai rahoton bacewar ta ga hedikwatar ‘yan sanda ta Alkaleri, a ranar 4 ga watan Agusta. Shafin Isyaku News Online isyaku.com ya samo.

Wakil ya ce wanda ya shigar da karar ya kuma bayyana wasu mutane biyu da ya ke zargin suna da hannu a bacewar yarinyar.

Ya ce daga baya an kama wadanda ake zargin kuma sun amsa laifinsu.

A cewarsa, da ake yi masa tambayoyi, shugaban wanda ake zargin ya amsa cewa yarinyar da ta bata budurwar ce kuma tana dauke da ciki wata hudu.

Kakakin ‘yan sandan ya ce wanda ake zargin ya ci gaba da bayyana cewa ya hada baki ne da mahaifiyar yarinyar da ta bace da kuma wanda ake zarginsa da shi inda ya kai wanda aka kashe zuwa Gombe domin a yi mata aikin zubar da ciki.

Ya ce yayin da suke garin Gombe wata mata ‘yar shekara 50 da ke zaune a unguwar Jekada Fari ta taimaka musu, inda aka yi wa wanda abin ya shafa allura da wasu abubuwan da ke haifar da zubewar ciki.

“Daga karshe a hanyarsu ta zuwa kauyen Mai’ari da ke daura da karamar hukumar Akko jihar Gombe, wadanda ake zargin biyun da muka ambata sun shake wanda aka kashen, wanda hakan ya sa ta mutu. 

“Hakazalika, an kona gawarra ta yadda ba za a iya gane ta ba tare da binne ta a wani kabari mara zurfi a wani daji da ke kusa da karamar hukumar Akko a jihar Gombe.

“A bisa wannan dalili, an fara bincike na farko; DPO Alkaleri ya ziyarci wurin, inda ya kai ta zuwa babban asibitin Alkaleri, inda likita ya tabbatar da mutuwarta,” inji shi.

Wakil ya ce Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Umar Sanda, ya bayar da umarnin a mika kararrakin biyu zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da cikakken bincike.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN