Yan sanda sun fara binciken fyade da aka yi wa jaririya mai shekara daya


Rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta fara gudanar da bincike kan zargin fyade da aka yi wa wata jaririya ‘yar watanni 18 tare da kashe wata yarinya ‘yar shekara 13 a jihar. Shafin labarai na Isyaku News Online isyaku.com ya samo.

A wata sanarwa da Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil ya fitar ranar Asabar a Bauchi, ya ce an kama wani mutum mai shekaru 59 a Duniya dangane da fyaden. 

Ya kara da cewa an kuma kama wasu mutane biyu da ake zargi da hada baki wajen kashe yarinyar mai shekaru 13.

Wakil ya ce mahaifiyar jaririn mai suna Nenkat Danladi ta kai kara a ofishin ‘yan sanda na Yelwa a ranar 8 ga watan Agusta.

Mahaifiyar ta shaida wa ‘yan sanda cewa ta hadu da wanda ake zargin a kan gadonta tare da ‘yarta da misalin karfe 11:30 na dare.

“Bayan kamar mintuna 30, mai shigar da kara ta gano cewa sashin ‘yarta na zubar da jini.

“Tawagar ma’aikata karkashin jagorancin DPO Yelwa ta garzaya da jaririyar zuwa asibitin koyarwa na ATBU Bauchi domin duba lafiyarta. An kama wanda ake zargin kuma an fara bincike sosai,” inji shi.

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN