Majalisar dokokin jihar Katsina ta zartar da kudirori 273 a cikin shekaru 23 – A hukumance

Majalisar dokokin jihar Katsina ta zartar da kudirori 273 a cikin shekaru 23 – A hukumanc


Majalisar dokokin jihar Katsina ta ce ta zartar da kudirori 273 daga shekarar 1999 zuwa yau, daga na Majalisa na farko zuwa na bakwai. Shafin labarai na Isyaku News Online isyaku.com ya samo.

Mataimakin shugaban Majalisar, Alhaji Shehu Dalhatu-Tafoki, ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa na kwanaki 2 da aka yi ranar Asabar a Kano.

Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da High Level Women Advocates (HILWA) ne suka shirya taron, tare da hadin gwiwar Gwamnatocin jihar Katsina da na tarayya, kuma ofishin kula da harkokin kasashen waje (FCDO).

A cewar Dalhatu-Tafoki, daga shekarar 2015 zuwa yau, Majalisar ta zartar da kudirori 130 daga cikin 273, kuma ta samu amincewar Majalisa ta shida da ta bakwai.

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN