Wata mata mai tabin hankali ta shiga hannun ‘yan sanda a ranar Litinin 1 ga watan Agusta a unguwar Kwame Nkrumah da ke birnin Accra bayan ta jefe wani saurayi har lahira. Shafin Isyaku News Online (isyaku.com) ya samo.
Hotunan da suka dauki mumunar lamarin, sun nuna mutumin kwance cikin jini a mahadar Nkrumah, wanda aka fi sani da Dubai.
An kama matar ne bayan da jami'an 'yan sanda suka samu kiran gaggawa kuma suka je wurin da lamarin ya faru a kan gadar sama.
Latsa ka kalli bidiyon yadda lamarin ya faru a ƙasa...
Them don arrest the mad woman👍 pic.twitter.com/Rb0u4iMTWB
— SIKAOFFICIAL🦍 (@SIKAOFFICIAL1) August 1, 2022