Gwamna Tambuwal ya karbi rahoton rikicin da ya jawo kisan Deborah Samuel


Kwamitin da gwamnatin jihar Sakkwato ta kafa domin ya binciko ainihin tashin hankalin da ya faru ranar 12 ga watan Mayu, 2022 a kwalejin Shehu Shagari ya miƙa rahotonsa ga Gwamna Aminu Waziri Tambuwal.

Tambuwal, bayan karɓan rahoton ya bayyana kiraye-kirayen da masu ruwa da tsaki ke yi na buɗe kwalejin, a cewarsa gwamnatinsa zata duba yuwuwar yin hakan.

The Nation ta tattaro cewa gwamnan ya umarci hukumar makarantar ta kira taro na musamman, wanda zai maida hankali kan shirye-shiryen yadda za'a cigaba da karatu.

Wane mataki Gwamnati zata ɗauka Kan rahoton?

Da yake tabbatar wa mutane cewa gwamnatinsa zata aiwatar da shawarwarin kwamitin, gwamna Tambuwal ya ce yin hakan zai kare faruwar makamancin abinda ya faru nan gaba, ba a kwalejin kaɗai ba har da sauran makarantu.

Mahaifiyar ɗalibar makarantar Kwaleji ta Shehu Shagari, Deborah Samuel, wacce aka kashe da zargin ɓatanci ta faɗi halin da ta shiga.

Matar mai suna, Alheri Emmanuel, ta ce ta samu labarin kisan ɗiyarta ta bakin ƙawayenta kuma ba zata taɓa mance wa da ranar ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN