DA DUMI-DUMI: 'Yan bindiga sun kai hari, sun raunata AIG 'Yan sanda, sun kashe wani dogarin cikin jami'an tsaronsa
A ranar Talata, 2 ga watan Agusta ne wasu ‘yan ta’adda suka yi wa ayarin motocin mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda (AIG) Audu Madaki na Bauchi kwanton bauna. Shafin labarai na Isyaku News Online (isyaku.com) ya samo.

Legit.ng ta ruwaito cewa a yayin wannan kazamin harin, ‘yan ta’addan dauke da makamai sun yi nasarar raunata AIG Madaki tare da kashe daya daga cikin jami’an tsaronsa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

An tattaro cewa AIG din yana kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Bauchi ne ‘yan ta’addan suka kaddamar da wannan harin a wani wuri tsakanin Barde da Jagindi a Kaduna, inda Madaki ya samu rauni.

An ce AIG yana karbar magani a wani asibiti da har yanzu ba a bayyana ba.

A yayin da aka tsaurara matakan tsaro a kusa da shiyya ta 12 mai hedikwata a Bauchi, an tura jami’an ‘yan sanda dauke da makamai zuwa yankin domin zakulo wadanda suka kai harin.

Kakakin hukumar shiyya ta 12, Thomas Goni, ya tabbatar wa jaridar The Cable faruwar lamarin, amma ya ce har yanzu rundunar ba ta samu cikakken bayanin abin da ya faru ba.

Goni ya ce:

“Har yanzu muna jiran cikakken bayanin lamarin.

“Kun san hakan bai faru a cikin ikonmu a nan ba; hakan ya faru ne a rundunar Kaduna don haka na kira layin Kaduna don samun cikakkun bayanai daga wurinsu."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN