Wani dan sanda ya mutu, wani kuma yana cikin mawuyacin hali sakamakon arangama da jami’an Sojoji a Legas


Akalla jami’in ‘yan sanda daya ya mutu, wani kuma an ce yana cikin mawuyacin hali sakamakon wata arangama da suka yi da sojojin Najeriya a yankin Ojo da ke jihar Legas a ranar Laraba, 3 ga watan Agusta.

Kamar yadda majiya mai tushe da ta zanta da LIB ta bayyana cewa, tawagar ‘yan sandan da ke aiki da sashin Tradefair ne ke bakin aiki a kofar CCECC da ke kan hanyar Legas zuwa Badagry domin kula da ababen hawa. A lokacin da suke bakin aiki, sun hana wasu motoci motsi domin yin hanya ga wata babbar mota mallakar kamfanin gine-gine CCEECC.

Sai dai daga cikin motocin da suka tsaya har da wata motar bas ta sojojin dauke da jami’ai 30 da ke kan hanyarsu ta zuwa makarantar horas da sojoji da ke Ojo. A cewar majiyoyin, jami’an sojan sun fusata ne da jami’an ‘yan sandan suka hana motarsu wucewa kawai domin su buda wa babbar motar hanyar wucewa yayin da su aka tsayar da su. An yi zargin sun sauko daga motar bas din suka fara kalubalantar jami’an ‘yan sandan da suka hada ASP, Insifetoci uku, da Sajan daya.

Al’amura sun lalace kuma ana zargin jami’an sun afkawa jami’an ‘yan sandan inda suka yi musu duka tare da yi musu rauni. Jami’an sojan da suka yi kaca-kaca da su sun yi awon gaba da Mujallar aje harsashi na bindigar ASP AK-47 dauke da harsashi har guda 25 tare da yin awon gaba da sufeto biyu tare da kwace bindigunsu.

An kai Sufeto da aka yi garkuwa da su zuwa sansanin sojin Ojo inda aka yi musu dukan tsiya.

Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na yankin E da ke Festac da jami’in ‘yan sanda na sashen ‘yan sanda na Tradefair sun ziyarci wurin inda suka tabbatar da an kai jami’an asibiti.

Abin bakin ciki, daya daga cikin Sufeto ya rasa ransa a lokacin da ake jinya a yammacin Alhamis, 4 ga watan Agusta. An ajiye gawar tasa a dakin ajiye gawa na Navy Reference dake garin Satellite domin adanawa da kuma tantancewa.

Da yake mayar da martani kan lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya ce

''Eh, akwai wani lamari da ya shafi sojoji da 'yan sandan mu, wanda ya kai ga mutuwar dan sanda guda, wani Insifeto. Hukumomin ‘yan sanda da na Sojoji suna aiki kafada da kafada don magance matsalar".

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN