A karon farko, Gwamna Wike da Atiku sun sa labule a gidan wani tsohon Minista


Ɗan takarar shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, sun gana a wani yunkuri da kawo karshen rikicin PDP a babban birnin tarayya Abuja.

The Cable ta fahimci cewa taron ya gudana ne a gidan tsohon Ministan yaɗa labarai kuma mamban kwamitin amintattu BoT, Jerry Gana.

Wata majiya ta bayyana cewa taron na yau Alhamis ya haufar ɗa mai ido kuma akwai taruka da zasu biyu baya na, "Ɗinke ɓaraka," waɗan da zasu maida hankali wajen kawo karshen saɓanin da ka faruwa a jam'iyya tun bayan zaɓen fidda gwani.

Majiyar ta ce:

"Nyesom Wike da Atiku Abubakar sun gana yau a gidan Farfesa Jerry Gana da ke Abuja, taron ya yi armashi, kuma akwai wasu tarukan da zasu biyo baya a kwanaki masu zuwa."

Taron ya zo ne awanni bayan kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP (BoT) ya kafa sabon kwamitin sulhu da zai kawo ƙarshen sabanin da ke tsakanin mutanen biyu.

Tun a ranar Lahadi, bayan gana wa da Wike, makusantansa da wasu gwamnonin PDP, Farfesa Gana ya ce zasu bayyana wa yan Najeriya duk halin da ake ciki idan an samu cigaba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN