Wata Kotun Majistare dake garin Damaturu a jihar Yobe ta yankewa wani Umar Alhaji Mustapha hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yari bisa samunsa da laifin aikata fyade da lalata da diyarsa mai shekaru 18 mai suna Fatima. Shafin Isyaku News Online (isyaku.com) ya samo.
Alkalin kotun mai shari’a Mohammed Bilyaminu ya yanke hukuncin cewa dukkanin abubuwan da ke cikin sashe na 390 da na 283 na kundin laifuffuka masu gabatar da kara sun tabbatar da su.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa, yayin da yake karanta shaidar, Alkalin ya bayyana cewa, PW 1, wani sufeton ‘yan sanda, a lokacin da yake ba da shaida, ya tabbatar da cewa mai laifin ya yi lalata da ‘yarsa da dama, ba tare da amincewarta ba wanda ya haifar da ciki. Sai dai yaron ya mutu bayan haihuwa.
Kotun ta bayyana cewa mai gabatar da kara ta tabbatar da cewa wanda ake tuhumar bayan ya yi wa diyar ciki, ya ba ta Naira 25,000 domin ta zubar da cikin wanda ta ki.
Haka kuma ita ma Fatima wadda aka yi wa ciki, ta kuma shaida cewa mahaifinta ya fusata matuka da ita bayan ya fahimci cewa tana da ciki kuma bata bi umarninsa na zubar da cikin ba, ya fara yi mata barazana.
Alkalin kotun, Mohammed Bilyaminu, ya bayyana wanda ake tuhuma da laifin lalata da kuma fyade a karkashin sashe na 390 da 283 na kundin penal code.
Ya yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar tare da biyan tarar dole na Naira 5,000 bisa laifin lalata da kuma shekaru 20 kan laifin fyade da tarar 10,000.
Kafin a yanke hukuncin, an baiwa wanda ake tuhuma damar neman a yi masa rahama, inda ya bukaci kotun ta yi adalci da jin kai.
"Ina da mahaifiya da ta tsufa da sauran wadanda suka dogara da su don kulawa," in ji wanda ake tuhuma.
Wanda aka yankewa hukuncin yana da kwanaki 30 don daukaka kara kan hukuncin cewar Alkalin.