Wani dan Achaba ya mutu wajen taya abokin sana'arsa rikici da Yan sanda


Wani Dan achaba da har yanzu ba a tantance ko wahe ba ya rasa ransa a wata arangama tsakanin masu tuka babur da ‘yan sanda kan wani hatsarin da ya afku a unguwar Abule-Egba da ke Legas. Shafin Isyaku News isyaku.com ya samo.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata a shafin sa na Twitter da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya samo.

A cewar Hundeyin, bayan wani dan karamin hatsari da ya hada da mota da babur ya afku a kan gadar Abule-Egba da misalin karfe 4:30 na yammacin (Talata) mahaya babura da yawansu sun fara tayar da hankali.

Ya ce ‘yan sanda sun isa wurin domin kwantar da tarzoma, amma masu baburan sun far wa ‘yan sandan da karfi.

“Muna da cikakkiyar masaniya kan tashe-tashen hankula a yankin Oko-Oba da ke jihar Legas. Hakan ya yi sanadiyar mutuwar daya daga cikin mahayan.

“An dawo da kwanciyar hankali a yankin. ‘Yan sanda a Oko-Oba suna nan a shirye don dakile duk wani tabarbarewar doka da oda,” inji shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN