Yan bindigan da suka sace Kwamishinan Nasarawa sun nemi kudin fansa N100m


Wadanda suka yi garkuwa da kwamishinan yada labarai na jihar Nasarawa Lawal Yakubu sun bukaci a biya su N100m a matsayin kudin fansa.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa an sace Yakubu ne a gidansa da ke karamar hukumar Nasarawa Eggon da yammacin ranar Litinin 15 ga watan Agusta.

Wata majiya mai tushe wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta tona cewa masu garkuwa da mutanen sun bayyana bukatarsu ne a ranar Talata

Ya ce tsagerun sun kira da misalin karfe 4:30 na yamma ta wayar daya daga cikin iyalan kwamishinan, sun sha alwashin ba za su karbi kasa da N100m kafin su sako shi.

A cewarsa:

“A gaskiya sun bugo waya da yammacin yau da misalin karfe 4:30 na yamma suka bukaci a ba su N100m kuma a lokacin da ‘yan uwan suka nemi ba da N3.5m sai suka kashe wayar cewa ba da gaske suke ba kuma suka dage cewa duk abin da ya yi kasa da N100m kawai a mance da shi. Sun kira lambar amma ba ta shiga.”

Ya zuwa yanzu dai ‘yan sanda tare da hadin gwiwar rundunoni da dama a hukumar ciki har da jami'an sashin yaki da masu garkuwa da mutane, jami’an soji, ’yan banga da mafarautan yankin sun fara kokarin mamaye dazukan yankin, inji SaharaReporters.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN