Tsananin kishi: Uwargida ta yanke al'aurar mijinta da ke barci da wuka bayan da ta yi gardama kan zargin zamba, duba yadda ta faru

Wata mata mai kishi ta yanke al'aurar mijinta da ke barci bayan da ta yi gardama kan zamba


Wata mata ta yanke al'aurar mijinta a lokacin da yake barci a farkon wannan watan. An yanke mata hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Kotun ta saurari yadda Jimmy Ngulube, daga Kapiri Mposhi a Zambiya, ya tashi da tsakar daren ranar 4 ga watan Agusta da ciwon mara bayan matarsa ta ya yanke masa al'aura.

Ya ga mamatarsa mai suna Chilufya tsaye a kansa rike da wuka jini na zuwa, kuma tana barazanar kashe shi.

Kafin su kwanta, Chilufya, mai shekaru 37, ta zargi mijin nata da yaudarar ta wanda hakan ya janyo cece-kuce. Da daddare ta farka ta yanke shawarar daukar fansa.

Jimmy, mai shekaru 43, ya kira dan uwansa wanda ya kai shi asibiti inda likitoci suka yi nasarar gyara mafi munin barnar.

An kuma sanar da ‘yan sandan yankin kuma an kai Chilufya gidan kaso.

A jiya, 26 ga watan Agusta, a Kotu, mai shari’a Kapiri Mposhi, Arnold Kasongamulilo, ya yankewa Chilufya hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari saboda ta raunata mijinta ba bisa ka’ida ba.

Chilufya ta roki kotun da ta yi mata sassauci, amma Alkalin kotun ya ci gaba da cewa ta hanyar kai wa mijinta hari tare da raunatata kamar yadda ta yi, ta nuna karara da niyyar kashe shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN