Rashin tsaro ya sa a rufe makarantun sakandire 75 a Zamfara – Jami’i


Akalla makarantun sakandire 75 a jihar Zamfara suke a rufe saboda matsalar tsaro. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Kampanin dillancin labarai na Najeriya NAN ta ruwaito cewa babban Sakatare a ma’aikatar ilimi Alhaji Kabiru Attahiru ne ya bayyana haka a Gusau ranar Asabar.

Ya na karanta sakon fatan alheri ga taron kwanaki biyu don aiwatar da manufar kasa kan ilimin jinsi (NPGE) wanda hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar tare da hadin gwiwar UNICEF suka shirya.

Attahiru ya lura cewa yawancin makarantun sakandaren mata ne da aka rufe tun watan Satumban 2021 sakamakon hare-haren da aka kai a wasu makarantun mata biyu a jihar.

Ya ce Gwamnatin jihar na aiki ba dare ba rana domin bude makarantun da aka rufe tun watan Satumban 2021 sakamakon barazanar da ‘yan bindiga suka yi musu.

Ya yi bayanin cewa Gwamnati ta bayar da umarnin rufe makarantun ne biyo bayan sace dalibai 75 da aka yi a Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kaya a karamar Hukumar Maradun.

Attahiru ya jaddada bukatar shigar da jami’an fage cikin tsara manufofin ilimi na kasa kan ilimin jinsi domin samun nasarar da ake bukata.

A nasa jawabin, mashawarcin hukumar UNICEF na jihar, Dr Ahmed Hashim, ya bayyana manufofin kwamitin da suka hada da duba abubuwan da aka samu a tarukan da suka gabata kan NPGE

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN