Ta faru: Dan Arewacin Najeriya mazauni kasar Algeria ya toma wa Bola Tinubu asiri kan yan Arewa


Wani dan Najeriya mazauni kasar Algeria, ya yi zargin cewa har yau akwai wasu Yan Arewacin Najeriya da dama da ke tsare a Kurkuku a jihar Lagos wanda ya samo asalin tun lokacin mulkin Bola Ahmed Tinubu a matsayin Gwamnan jihar Lagos. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Duk da yake bai ambaci sunansa ba, sai dai ya aike wa shafin labarai na isyaku.com sautin murya na WhatsApp a zaman martani biyo bayan wani labari da shafin ya wallafa da ya ambaci Bola Tinubu.

Ya yi zargin cewa tabbas shi ya san cewa akwai asalin yan Arewacin Najeriya mazauna birnin Lagos da har yanzu suke tsare a Kurkuku, lamari da ya samo asali tun lokacin mulkin Bola Ahmed Tinubu.

Sai dai duk da wannan zargin, bai ambaci irin laifuka da wadannan yan Arewa suka yi har aka yi masu irin wannn dauri a Kurkuku ba idan har zargin ya zama gaskiya..


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN