Yan bindiga sun sake sare hannayen wani mutum a jihar Zamfara bayan ya hanasu satar kaji a gidansa


Wani mazaunin jihar Zamfara mai  suna Samaila Muhammad ya shiga hannun wasu ‘yan bindiga a jihar. 

Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa lamarin ya faru ne bayan ‘yan bindigar sun kai farmaki gidansa da ke unguwar Walo a karamar hukumar Kaura Namoda a jihar.

Dan uwan ​​Samila, Abdullahi Mohammed, wanda ya bayyana cewa an datse hannayen sa a yayin harin, ya shaida wa Daily trust cewa;

“A halin yanzu ni da dan uwana Samaila muna kwance a asibiti saboda nima na samu karaya a hannu da kafa.

“Da misalin karfe 11:30 na dare ne ‘yan ta’addan suka kai hari. Sun tilasta kansu shiga cikin gidanmu, suka fara neman inda muka ajiye dabbobinmu. Muka fara jin hayaniya muka damko fitilun mu muka fito daga dakunanmu domin jin me ke faruwa. Na ga daya daga cikin masu dauke da makamai yana kokarin kwace kajin mu, sai na kunna masa fitilar hannu.

“Ya yi harbin kan hanyata duk da cewa harsashin bai same ni ba. Na yi saurin matsawa daga inda na tsaya. Suka fara dibar kaji, da yayana ya kalubalance su, sai daya daga cikinsu ya fito da adda ya yanke hannunsa daya, kafin ya yi yunkurin tserewa harin da makamin ya yanke dayan hannun shi ma.

“Al’ummarmu sun sha fama da munanan hare-hare a baya kuma mun sha wulakanci da dama ciki har da fyade da ake yi wa matan mu. A halin yanzu muna karbar magani kuma muna samun sauki bayan mun shafe kwanaki a wurin jinya."

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN