Sheikh Abubakar Giro Argungu bai rasu ba - Wani Dansa


Shafin labarai na isyaku.com ya samu tabbacin cewa Sheikh Abubakar Giro Argungu bai rasu ba, yana nan da ransa cikin rahamar Allah.

Biyo bayan jija-jita da ya bazu a kafofin sada zumunta daga yammacin ranar Laraba 17 ga watan Agusta cewa Shehun Malamin ya rasu.

Shafin labarai na isyaku.com ya zanta da daya daga cikin 'ya'yan Sheikh Giro wanda ya tabbatar wa shafin ranar Alhamis 18 ga watan Agusta cewa Malam yana raye, kuma ya nada faifen bidiyo da ya karyata jita-jitan rasuwarsa. 

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN