Rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran jami’an tsaro a jihar Kebbi sun gudanar da wani zagayen baje kolin karfin tsaro da sintiri a cikin garin Birnin kebbi da kewaye ranar Juma'a 19 ga watan Agusta 2022. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Kwamishinan Yan sandan jihar Kebbi CP Ahmed Magaji Kontagora ya shirya tare da jagorantar baje kolin karfin da jami'an tsaro ke da shi na fuskantar makiya zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'ummar jihar Kebbi bisa bayanan da ya yi wa manema labarai a ofishinsa jim kadan bayan gudanar da lamarin.
Jami'an Yan sanda, soji, Nigeria security and civil defence corps NSCDC, National drug law enforcement agency NDLEA, Nigerian immigration service NIS, da Nigerian customs service NCS na cikin baje kolin karfin tsaro da ya gudana.
Latsa nan ka kalli bidiyo:
Latsa nan ka kalli Hotuna: