Jama'a sun yi wa barawon wayar salula dukan ajali, sun kone gawarsa bayan sun ceto wanda barawon ya sace masa waya


Yan sanda a Bayelsa a ranar Alhamis sun gargadi mazauna garin kan daukar doka a hannunsu. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Gargadin ya biyo bayan kashe wani da ake zargin barawon waya da wasu mutane suka yi a Yenagoa ranar Laraba.

Fusatattun mazauna unguwar Green Villa Road a Yenagoa sun ceto wani matashi daga barawon waya da ya yi kokarin kwace masa wayarsa da bindiga.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa mazauna yankin da suka ceto wanda ake zaton an kashe sun yi wa maharin hukuncin Yan dani yayin da aka kona shi kafin ‘yan sanda su isa wurin.

Mazauna yankin sun ce wasu mutanen da ke wurin sun yi wa ‘yan sanda kira na gaggawa, amma jinkirin da aka samu ya kai ga aiwatar da shari’ar daji.

Da yake mayar da martani kan lamarin, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya yi Allah-wadai da wannan aika-aika tare da bayyana takaicin yadda jami’an tsaron suka isa wurin a lokacin da aka kona wanda ake zargin har lahira.

Ya bukaci jama’a da su guji daukar doka a hannunsu.

Ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN