Sarki Sanusi: Dole ne matasa su yi tambayoyi, su nemi amsoshi daga jami’an Gwamnati kan yadda suke jagorantar al'umma


Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, ya bukaci matasan Najeriya da su tashi tsaye wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, su rika yin tambayoyi, da neman amsoshi, da kuma dora masu rike da mukaman Gwamnati hukunci. Shafin isyaku.com ya samo.

NAN ta ruwaito cewa Sanusi, wanda kuma shi ne Halifa na yanzu, na kungiyar Tijjaniya ta Najeriya, ya bayyana haka ne a Legas ranar Lahadi a lokacin da yake jawabi a wani taron wasan kwaikwayo da ya nuna rayuwarsa da zamaninsa.

Wasan mai suna: “Emir Sanusi: Truth in Time”, Ahmed Yerima, Farfesa a fannin wasan kwaikwayo a Jami’ar Redeemer, Ede ne ya rubuta shi, kuma Mista Joseph Edgar, Babban Shugaban Kamfanin Somolu Productions ne ya shirya shi.

“A matsayinmu na ‘yan kasar nan, makoma tana hannunmu; idan ba a kula ba, babu kasa ga matasa da yadda kasar nan ke tafiya.

“Idan har Ministoci da Kwamishinoni da Gwamnoni da shugabannin Kananan hukumomi suka yi aikinsu yadda ya kamata, Najeriya za ta yi kyau".

“Yi tambayoyi, fayyace batutuwa, kar a share al'amura a ƙarƙashin kafet.

"Sau da yawa, ana suka na da yin magana a bainar jama'a don nuna adawa da manufofin Gwamnati, amma abin da mafi yawan mutane ba su sani ba shi ne yadda na yi magana da wadannan jami'an Gwamnati a sirce wani lokaci na tsawon watanni ko shekaru kafin in fito fili in bayyana su," in ji Sanusi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN