Da zafi-zafi: Sojin sama sun sheke dan ta'addan da ya kitsa kai hari kan tawagar Buhari a Daura


An kashe shugaban ‘yan ta’adda, Abdulkarim Faca-Faca, wanda ke cikin wadanda suka kitsa harin da aka kai wa ayarin motocin shugaban kasa Muhammadu Buhari a Katsina.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an kashe shi ne tare da ‘yan kungiyar sa guda 8 a ranar Asabar 6 ga watan Agustan 2022.

Majiyoyi sun ce, an kashe shi ne yayin wani farmaki da rundunar sojojin saman Najeriya ta kai wani samame kan maboyar ‘yan ta’addan a kauyen Marina da ke karamar hukumar Safana a Katsina.

Wata majiya daga tushe ta ce 'yan ta'adda da dama sun samu raunukan harbin bindigogi, sai daia abin takaici sun yi nasarar tserewa. Ta kuma ce, a yayin wannan aikin, an lalata shanun da barayin suka sato.

Dan majalisa mai wakiltar Safana a majalisar dokokin jihar Kaduna, Abduljalil Runka, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewar Runka:

“Gaskiya ne. Da yammacin ranar Asabar ne sojojin saman Najeriya suka kai samame yankin inda suka ci gaba da fatattaka har safiyar yau. An kashe Abdulkarim Faca-faca da yaransa takwas a harin. An binne su ne a Marina, garinsu da safiyar Lahadin nan.”

'Yan Ta'adda Sun Sheka Barzahu Yayin Wani Artabu da Sojoji A Jihar Borno

Mazajen Sojojin Najeriya sun yi nasarar daƙile harin wasu da ake zargim mayaƙan ƙungiyar ta'addanci ISWAP ne a garon Monguno, jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.

The Cable ta tattaro cewa yan ta'addan sun shiga garin ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare ranar Jummu'a tare da motocin yaƙi, Babura da muggan makamai, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Wani jami'in hukumar tattara bayanan sirri ya shaida wa Zagazola Makama, masani kuma mai sharhi kan harkokin tada ƙayar baya cewa Sojoji sun tarbi yan ta'addan, suka yi musayar wuta har karfe 11:30 na dare.

Rahoto ya nuna cewa a wannan artabu da dakarun sojin Najeriya ne da yawan yan ta'adda suka sheƙa barzahu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN