Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta cafke wani soja mai shekaru 90 mai ritaya, Usman Adamu, a unguwar Mailalle da ke Sabon Birni, a cikin garin Sokoto bisa zargin sa da safarar miyagun kwayoyi. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
NAN ta ruwaito cewa Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na NDLEA, Mista Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Babafemi ya ce wanda ake zargin wanda aka kama a ranar 3 ga watan Agusta, an kama shi da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 5.1, a lokacin da aka kama shi.
Babafemi ya ce shugaban hukumar ta NDLEA, Brig.-Gen. Buba Marwa (rtd) ya yabawa hafsoshi da jami’an MMIA, Sokoto, Zamfara, Kogi, Delta, Enugu, da Kaduna Commands bisa wannan kwazon da suka nuna.
Ya ce Marwa ya bukaci su da sauran sassan kasar nan da su ci gaba da mai da hankali da kuma lura