Rashin tsaro: Gwamna Bagudu ya aika wani muhimmin sako ga al'ummar jihar Kebbi


Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya bukaci ‘yan Najeriya da su tuba su kara himma wajen yin addu’o’i domin kawo karshen matsalar rashin tsaro da ke addabar al’umma. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Bagudu ya yi wannan roko ne a wani walima (Dinner) da aka shirya domin bikin “Kebbi @ 31”, wanda aka gudanar a dakin taro na Presidential Lodge, Birnin Kebbi ranar Asabar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa walima da Gwamnatin jihar Kebbi ta shirya, ta zabo Malamai (Malaman Musulunci) daga bangarori daban-daban na addinin Musulunci domin yin wa’azi tare da gabatar da addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya a fadin Najeriya.

Bagudu, wanda ya samu wakilcin Alhaji Babale Umar-Yauri, sakataren Gwamnatin jihar Kebbi (SSG), ya ce jihar ta yanke shawarar yin bikin cika shekaru 31 a wata hanya ta daban.

“Mun yanke shawarar gayyatar Malamai domin su yi mana wa’azi, tunatar da mu game da Allah Madaukakin Sarki da kuma yi mana addu’ar samun zaman lafiya a fadin Nijeriya,” inji shi.

Gwamnan ya koka da yadda ‘yan fashi da yan ta'adda da kuma masu garkuwa da mutane, da wasu munanan dabi’u da ke kutsawa cikin Najeriya, yana mai tabbatar da cewa da addu’a nan ba da dadewa ba za su zama tarihi.

Da yake yabawa Malamai bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen samun nasarar jihar, Bagudu ya kuma yi kira gare su da su ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Tun da farko, Malamai da dama da suka yi wa'azi a walima, sun tunatar da mutane da kuma shugabanni wajibcin kula da irin nauyin da ya rataya a wuyansu.

NAN ta ruwaito cewa Malaman sun hada da Sheikh Abbas Muhammad-Jega, wanda Sheikh Usman Adam-Jega ya wakilta; Sheikh Umar Malisa, wanda Sheikh Tijjani Muhammad ya wakilta; Sheikh Basiru Musa da Sheikh Abdur-Rahman Isa-Jega.

Yayin da suke daukar nassosinsu daga Alqur'ani da Hadisi, Malamai sun lissafta wasu halaye na shugaba da suka hada da tawali'u, tuntubar juna kafin yanke hukunci, sassauci da adalci.

Malaman sun jaddada bukatar mabiyan su kasance masu biyayya da mutunta dukkan hukumomin da aka kafa domin baiwa shugabanni damar sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN